Click here to skip to this page's main content.

New to the Open Library? — Learn how it works
Last edited by Shuraihusman
September 24, 2017 | History

NAMIJIN GASKE part 1B 1 edition

By unknown author
NAMIJIN GASKE part 1B

Read

No readable version available.

Borrow

Try a WorldCat search?

Buy

Add an ISBN to link to booksellers

Lists

You could add NAMIJIN GASKE part 1B to a list if you log in.
Sheesh. There's no description for this book yet. Can you help?
There is only 1 edition record, so we'll show it here...  •  Add edition?

NAMIJIN GASKE part 1B
Shuraih Usman

Published 2017 by Shuraih 99% in Nigeria .

Table of Contents

<img src="http://shuraih.faceblog.id/files/namijin-gaske.jpg"/>NAMIJIN GASKE
Littafina daya 1
Marubuci:- Shuraih Usman
Typing:- Shuraih Usman
Tel. 08133209890
Part A
.
Doka, banyarda wani yayi copy ko ya sarrafa wannan labari ta
ko wace hanya batare da izni na ba. Dafatan za'a kiyaye
Copyright
Shuraih Usman
.
Kimanin shekaru ashirin da suka gabata a birnin tehran , birnin tehran babban birnine wanda mutanen cikinsa yawancin sana'arsu itace Noman kayan Abinci iri iri,
Kasuwar garin nacine a duk mako. Kuma daga wasu garuruwan sukan ziyarci wannan kasuwa a duk makon da zaici,
.
Al'umman birnin tehran ma'abota son zaman lafiya ne, A yayin da adalin sarkinsu hinzur bin humas, ya tsaya tsayin daka wajen yada zaman lafiya a duk sassan birnin
.
Sarki hinzur babban sadaulkine wanda duk ilahirin nahiyar babu sadauki kamarsa.
Ya kasance yana da wani dan uwa mai Suna Humaiz bin Humas .
Shi Humaiz yan uba suke da hinzur wannnan tasa ya kullaci hinzur sosai a cikin zuciyarsa,
Wacce har takai ta komo So yake yaga bayan sarki hinzur sannan ya kwaci mulkinsa. Duk da kuwa alokacin matsayin wazirin tehran yake.
Duk wani bakin ciki da hassada gami da kyashi da yake wa sarki hinzur bai taba Nuna wa a gabansa ba, hasalima irin biyayya da so da kauna da yake nuna wa hinzur kai kace tamkar da gaskece amma na ciki na ciki
.
Waziri humaiz yasan bazai iya tarar sarki hinzur gaba da gaba ba, don kuwa linzami tafi karfin bakin kaza.
Hakan tasa yaje ya samu wasu yanfashi a wajen gari cikin wani kungurmin daji , nan take ya zayyane masu bukatarsa na son su taimakeshi su hada karfi da karfe, don su kawar da sarki hinzur a ban kasa.
.
Shugaban yan fashin mai suna kallabu ya dubi waziri humaiz bayan sun gama sauraron bayaninsa yace da shi ,
"Yakai wazirin birnin tehran hakika kazo mana da abinda muka dade muna jira tsawon wasu watanni, lallai kasani wannan taimako daka nema daga wajenmu tamkar mune muka nemi taimako daga gareka"
Waziri najin haka sai ya cika da tsananin mamaki sannan ya dubi kallabu yace "shin kai kuwa wannan shugaba ta yanfashi meye dalilin ka na fadin hakan"
Nan take Kallabu ya bushe da dariya saida yayi mai isarsa sannan ya dubi
Waziri humaiz yace da shi "yakai humaiz kai sani cewa mun dade muna son ganin bayan sarki hinzur bisa takura mana da yayi, lallai zamu taimakeke ba tareda mun karbi ko kwandalarka ba, Abin dana ke jimana shakka iyace ta yaya zamu ratsa har mu shiga gidan sarki hinzur .
Humaiz najin wannan tambayar sai yayi murmushi sannan yace" indai maganan shiga gidan sarkine toh lallai ina tabbatar maku shan ruwa ma ya fishi sauki a wajena, domin kuwa akwai wani hadimina da zansa ya jagoranceku har zuwa turakar sarki"
."
Koda yamma tayi sai shugaban yanfashi da yaransa kimanin su dari biyar, sukayi shiri irin ta fatake sannan suka tasamma birnin tehran
.
Koda suka iso bakin kofan birnin tehran sai masu tsaron kofa suka tsaida su,
Wani badakare wanda da alamu shine babba acikin dakaru masu tsaron kofan garin ya kusanto gaban wayannan yanfashi wayanda suka yi shirin fatake ya tambayesu
"Yaku wayannan ayari su waye ku , sannan Me ke tafe da ku izuwa wannan kasa tamu mai tarin daraja"
.
Koda jin haka sai kallabu wanda yabadda kamanninsa ta hanyar nade wata katuwar rawani a kansa ya dubi wannan dakare yace
"Yakai wannan mai tsaron kofan kasani mu fatakene sannan bada niyyar komai muka iso wannan birnin ba face don kasuwanci"
Shugaban masu tsaron kofan yace
"Wacce irin haja kuka dauko"
Kallabu yai nuni da hannunsa ga bayansa wasu rakumane a kalla sunkai hamsin dauke da manyan sundukai a bayansu,
Sarkin kofa ya iso gaban rakumi daya sannan ya bude sunduki daya daga cikin sundukannan ,
Babu komai aciki face kayan masarufi kama daga dangin zinare har zuwa kan su murjani da yakutu.
Nan take shugaban masu tsaron kofa ya bada umarni da a bude musu kofa su wuce
.
Koda suka shigo birnin tehran basu zame ko ina ba sai cikin kasuwan garin , inda suna isa suka tarar da wani hadimin waziri humaiz .
Wannan hadimi yai masu jagora izuwa wata babban gida ta sirri wacce ta kasance mallakin waziri humaiz ne.
*****
Can cikin talaitainin dare kuwa dukkan wayannan yan fashin sunyi mugun shirin yaki. Kai kace yakin duniya zasuje
Gama kimtsawarsu keda wuya sai hadimin waziri humaiz daya jagoranci su kallabu izuwa wannan gida ta sirri ya shigo garesu
.
Sunan hadimin KAMSAS kuma shine amintaccen hadimin waziri humaiz
Kamsas ba karamin hatsabibi ba ne don kuwa duk cikin hadiman waziri babu wanda yake matukar ji dashi tamkar kamsas
.
Nan kamsas ya dubi kallabu yace " ya shugabana Muna iya tafiya yanzu"
.
Ta bayan gari suka bi gudun kar wani yaji takun sawaye ya yawaita ya farka daga barci.
Ba a dadeba suka fara hango kofan gidan sarki, masu gadi na nan sai zagaye suke ta ko ina
Koda kallabu yaga haka sai ya dubi kamsas
"Shin ta ya ya kake ganin zamu ratsa wayannan da karu masu tsananin yawa wayanda na tabbata ko munyi nasarar gamawa da toh sai nayi asarar dakaru masu yawan gaske .daga karshe kuma in muka shiga gidan sarki ragowan sauran dakarunsa su karisamu.
Kamsas na jin haka sai yayi murmushi sannan yace "ya shugabana kai dai ka tsaya zakaga ta yadda zamu samu nasarar shiga gidan kuma batare da mun raunata badakare ko guda daya ba"
.
Kamsas na gama fadin haka sai ya rike hannun shugaban yafashi kallabu sannan yace mai yai ma yaransa umarni da kowa ya rike hannun juna,
Cikin dan kankanin lokaci sai gaba daya yan fashinnan suka rirrike hannuwan yan uwansu.
Nan take kamsas ya fara fadin wasu kalmomi daga cikin yaren girkawa,
Take sai wata guguwa bayyana , koda bayyanar guguwar saita nufosu tana zuwa wajenda suke sai ta suresu tai sama da su
*****
Marubuci:- Shuraih Usman
Hakkin mallaka (m) Shuraih Usman
Company:- Shuraih 99%
(c) shuraih Usman 2017
Typing:- shuraih 99%

ID Numbers

Open Library
OL26378844M

History Created September 24, 2017 · 2 revisions Download catalog record: RDF / JSON

September 24, 2017 Edited by Shuraihusman Edited without comment.
September 24, 2017 Created by Shuraihusman Added new book.