Click here to skip to this page's main content.

New to the Open Library? — Learn how it works
Last edited by Shuraihusman
September 24, 2017 | History

NAMIJIN GASKE 1 1 edition

By unknown author
NAMIJIN GASKE 1

Read

No readable version available.

Borrow

Try a WorldCat search?

Buy

Add an ISBN to link to booksellers

Lists

You could add NAMIJIN GASKE 1 to a list if you log in.
Rats. There's no description for this book yet. Can you help?
There is only 1 edition record, so we'll show it here...  •  Add edition?

NAMIJIN GASKE part 1A
Shuraih Usman

Published 2017 by Shuraih 99% in Nigeria .

Table of Contents

NAMIJIN GASKE
Littafina daya 1
Marubuci:- Shuraih Usman
Typing:- Shuraih Usman
Tel. 08133209890
Part A
.
Doka, banyarda wani yayi copy ko ya sarrafa wannan labari ta
ko wace hanya batare da izni na ba. Dafatan za'a kiyaye
Copyright
Shuraih Usman
.
Saurayi ne kyakkyawa ma'aboci kyawun fuska, wacce duk ya
macen da yai arba da ita sai kware masa.
Babu komai ajikinsa face wata falmara ta fatan zaki, falmarar
ba'a rufe madannin ta ba, hakan tasa dukkan ilahirin kirjinsa a
bayyane yake a fili,
Gaba daya kirjinsa waje yake, hakan ce ta bayyana surar kirar
jikinsa, ko ina ajikinsa a murmurde suke, a yayin da wasu
guruna suka bayyana bisa tumbinsa kai kace baya cin abinci ne.
A kasansa kuwa wata gajeriyar wando ce iya guiwa , ya sanya
,rike yake da gabjejiyar itace a hannunsa .
Yana tafe yana waige waige koda zaici karo da abinda ya fito
nema, kai da gani kasan wannan kyakkyawan saurayin farauta
ya fito yi,
.
Yana tafiya yana gunaguni a cikin zuciyarsa kuwa tunani yake
"wai yayane anya wannan karon da sa'a kuwa, Ni dana ke fitowa
farauta na kamo manyan namun daji masu ababen al'ajabi,
Kuma cikin kwanaki biyu rak nake kamosu sannan na tasamma
gida,amma wannan karon gashi har na tasamma kwanaki hudu
amma ko tsuntsu banyi arba da shi,
Maganar tasa ta katse a dalilin wani gurnani daya ji,
Ai koda yaji wannan gurnanin sai ya cika da farin ciki ainun
bisa ganin wahalarsa tazo karshe,
.
Gurnanin yaci gaba da kusanto shi, ta cikin wata duhuwar
sarkakiya ne gurnanin ke fitowa.
Nan ya tasamma wannan sarkakiyar, koda ya rage baifi saura
kadan ya karisa ba, kawai gani yayi wata murgujejiyar damisa
ta fito daga cikin sarkakiyar ta bayyana a gabansa,
.
Ya dubi wannan damisar sai ya ganta lafceciya, sai yayi
murmushi sannan a fili yace da alamu dai yau zan koma izuwa
gida da karamin nama.
Itako damisar sai dalalar da yawu take bisa kasa,
Yau kwanakinta kusan goma kenan bata dandani Nama ba ,
kullum sai ciyayi take ci
Toh yau ga tsuntsu daga sama gasasshe,
.
Mayunwaciyar Damisar tayi ruri sannan ta fada kan jarumin
saurayin ,
Nan suka zube kasa gaba dayansu
Damisar tana bisansa sai kokarin farke wuyansa take da
hakoranta, a yayin da shi kuma saurayin ya rike habarta da
hannunsa, sannan yasa kafa ya taka ta , take damisar tayi sama
yadda kasan an dauketa da majaujawa , koda damisar ta fado
bisa kasa sai tayi wata irin kara sakamakon jin zafin takun da
saurayin yamata .
.
Saurayin ya mike tsaye sannan yayi wata irin tsayuwa irin na
Mazan kwarai,
.
Damisar na ganin haka sai ta kara dumfaro shi da nufin tai tsalle
ta diram mai a wuya,
Koda tai tsallen da nufin ta fada akan wuyansa sai kyakkyawar
saurayin ya sanya hannunsa guda . Ya rike mata makoshi, sai
gashi murgujejiya kuma lafceciyar damisar na wutsil wutsil a
hannunsa kai kace, masunci ne ya kama kifi.
.
Take saurayin ya daga damisar sama sannan yai jifa da ita ,
koda yai jifa da ita sai taje ta gwaru da wani babban bishiya ,
take bishiyan ya fadi rikica,
Wannan damisar ko shurawa batai ba,
Kyakkyawan saurayin yazo gaban gawar damisar , ya tsugunna
da nufin ya sabata a kafadarsa yayi gida,
.
Ba zato babu tsammani kawai sai ya fara jin Dirdir gowan wasu
abubuwa a bayansa,
Koda ya juya don yaga mene wannan.
Anan ne yayi arba da su,
Wasu gabza gabzan Arnan daji ne,
Su wayannan arnan dajin suna sanyene warki na fatun
mesa,dukkanninsu kamanninsu da fasalin surar jikinsu dayane ,
Lafta lafta ne ma'abota tarin damatsa babu kaya a jikinsu face
wannan warkin na fatan mesa,
.
Daya daga cikinsu yazo gab da wannan kyakkyawan saurayin
yace " yakai wannan kyakkyawan saurayin kayi sani cewa ka
aikata babban kuskure a garemu wanda hukuncinka shine kisa
mafi muni"
.
Cikin gadara saurayin ya dubi arnan dajin nan wayanda
adadinsu yakai dari yace
"Ku sani ni bansan mai na aikata a gareku ba da har zaku yanke
wannan hukuncin akaina "
.
Shugaban arnan dajin ya daka masa tsawa sannan yai nuni da
dan yatsansa izuwa ga gawar damisar nan yace "shi wannan
damisar daka hallaka , shine mafi kusanci ga abin bautarmu,
duk wata bukata da muke da ita ga abin bautarmu muddin muka
kama kafa da wannan damisar toh take abin bautarmu yake biya
mana buka tunmu.
.
Kasani yakai wannan gafallallen saurayi, ako wacce rana mun
kasance muna farauto ma wannan damisar mutun daya don tayi
kalaci da shi,
Haka muka kasance muna yi har tsawon wasu shekaru,
Kwatsam sai gashi an wayi gari mun fita nemo wa damisar abin
kalacinta, har muka debi tsawon lokaci bamu dawo ba,
Hakan yasa yunwa ya addebeta ta fito neman wanda tsautsayi
ya kasa dashi, sai gashi ka kashe mana ita,
Abisa wannan mummunan zunubin daka aikata mana ne
shugabanmu Boka Abulzulmu ya turo mu damu yimaka kisa irin
ta wulakanci ,
Don haka ina umartarka daka bani kanka cikin maslaha nai
maka kisan sauki, "
Koda jin haka sai kyakkyawan sauyarin ya tuntsire da dariya,
sai da yayi mai isarsa sannan yace "Ashe ma mugun iri na rage
A doron kasa kunga yanzu babu wata rai dazata kara salwanta a
dalilin wannan Damisar"
Yana rufe bakinsa sai shugaban arnan dajin yayi kukan kura
sannan nufo kan saurayin, hannunsa rike da sharbebiyar takobi,
Koda yazo daf da saurayin sai ya kai mai sara da nufin ya cisge
mai kai, cikin zafin nama saurayin ya sunkuya saran tabi iska,
.
Kafin shugaban arnan dajin ya sake kaimai wani saran . Sai
kyakkyawan saurayin yayi wuf cikin zafin nama ya kirba ma
shugaban arnan dajin dundu a baya,
Nan take shugaban arnan dajin ya kwalla kara sannan yayi taga
taga tamkar zai fadi amma sai ya tirje, take ya furzar da jini
daga bakinsa.
Saurayin baiyi kasa a guiwa ba ya kama kan shugaban arnan
dajin ya murde, karan karyewan kashi ta bayyana, duk wata
gaba ta daina motsi ajikin shugaban arnan dajin,
.
Kyakkyawan saurayin yai jifa da gawar izuwa ga sansanin da
arnan dajin ke tsaitsaiye,
.
Wasu arnan daji biyu suka cafe gawan amma sabida karfin jifan
da saurayin yayi da gawan sai da suka zube kasa gaba dayansu.
.
Koda arnan dajin suka ga abinda saurayin ya aikata ga
shugabansu sai dukkaninsu suka yi kururuwa sannan suka zare
makamansu, nan suka rugo da gudu da nufin su isa wajen da
saurayin yake su gididdibashi gida gida.
Shi ko saurayin koda yaga sun nufoshi sai yayi murmushi
sannnan ya gyara tsayuwansa.
Koda arnan dajin suka kariso wajenda saurayin yake sai sukai
mai rubdugu.
Shi ko saurayin koda yaga haka sai ya sanya dukkan karfinsa ya
tarwatsasu, hohoho!!
Da mutum yana wajen yanaganin yanda mutun daya ya gagari
daruruwan mutane lallai daya tabbatar da cewa wannan
kyakkyawan saurayin ya cika NAMIJIN GASKE mai tarwatsa
maza.
.
Arnan dajin sai kai masa sara da suka suke , shi ko ya wanzu
yana mai zullewa da gociya,
Babu abin da zaibaka mamaki da saurayin face ganin ko
makami babu a hannunsa.
A duk lokacin daya samu arnen daji ya kirba mai naushi ko
dundu. Nan take zakaga mutun ya fadi wanwar akasa ko
shurawa bazai yiba
.
Sai da aka dauki tsawon lokaci ana wannan fafatawan inda
saurayin yai ta ragargazar arnan dajin ,
Har ya samu nasarar karkashesu gaba daya.
Sannan ya dauki gawan damisar ya azata bisa kafadansa, yayi
tafiyarsa
.
Tafiya yake har ya kawo bakin wata bukka , sannan yayarda
gawar damisar a kasa,
.
Ya nufi wani turki ya zauna ,
Zamansa keda wuya sai waya kyakkyawan mace ta fito daga
cikin wannan bukkan
.
Wannan matar zata kai shekaru hamsin da doriya amma in
kaganta kace yar shekara talatin da wani abune.
Matar ta dubi saurayin tace dashi
"MUHAISIN sai yau kadawo"
Jarumin saurayin da aka kira da muhaisin ya dubi wannan matar
yace
"Ummi na kenan kisani dadewar danayi ta samo asaline daga
rashin samun dabbar danake nema"
.
Wannan matar sunan ta hamasiya sun kasance suna rayuwa
acikin wannan kungurmin dajin shekara da shekaru ita da danta
muhaisin
Tun muhaisin bai mallaki hankalin kansa ba
Ya taso ya tsinci kansa acikin wannan daji,
Tun baifi shekaru tara a duniya ba mahaifiyanshi hamasiya take
ganin ababen al'ajabi a tattare da shi.
Don alokacin baifi shekara tara a duniya ba amma sai taga ya
fita da nufin zai je farauta, in ya fita kuwa baya da wowa sai
bayan kwanaki biyu
.
Nan zai dawo da manyan namun daji wayanda ko rikakken
mafarauci ma sai yayi da gaske kafin ya kama irinsu
.
Tun hamasiya tana al'ajabi har tazo ta daina ,bangaren jarumta
kuwa duk yawan abokan gaba tarwatsasu yake, kuma shi baya
fada da makami don ko dabbobi ma wuyanzu yake murdewa.
Tun da yake a rayuwarsa bai taba yin yaki ko fada da makami
ba da zallan karfin damtse yake yakan ayari guda na yan fashi,
da kuma gungun yan harin sumame.
Haryanzu da kwai wasu yanfashi dake tarkonsa
Su yan fashin sun riga da sunsan yafi karfinsu shi yasa da sun
hadu sai kaga yan fashin sun ruga a guje .
Ace warsu wai lokacin haduwarsu baiyiba tukun idan lokaci
yayi su da kansu zasu nemeshi,
.
Alokacin da muhaisin ya mallaki hankalin kansa sai ya fara
tambayar hamasiya mahaifinshi
Hamasiya takance da shi mahaifinsa ya rasu.
.
Alokacin da hamasiya tazo gaban muhaisin don taga alamun
gajiya ajikinsa sai taga gefen damtsensa na zubar da jini , nan
da nan hankalinta ya tashi ta yagi wani kyalle dake rataye bisa
wannan turkin , sannan ta kama hannun muhaisin tana daure
mai wannan raunin
.
Nan ta tambayeshi meya ji mai wannan rauni,
Bai boye mata komai ba , ya labarta mata artabonsa da arnan
daji
.
Koda hamasiya ta saurari labarinsa sai nan da nan kwalla ya
cika mata idanu, koda muhaisin ya lura da yanayin da
mahaifiyarsa ta shiga sai ya ce" yake ummina shin ina dalilin
zubar da hawayenkinnan , "
Hamasiya tayi sauri ta share kwallan tace" yakai dana kayisani
bako maine ya sanya ni zubda hawaye ba face tuno da
mahaifinka da nayi, Lallai ka gaji mahaifinka dana."
.
Muhaisin najin haka sai ya durkusa bisa guiwowinsa yace" Na
rokeki ummina daki sanar dani labarin mahaifina da kuma
dalilin dayasa muke rayuwa a cikin wannan kungurmin dajin"
.
Koda jin wannan tambayan sai Hamasiya ta mike tsaye sannan
ta nufi wannan bukkar koda tazo gab da bukkan sai ta tsaya ta
dafa bukkan da hannu daya sannan ta juyo ta dubi muhaisin
tace " yakai dana hakika yau kayi mani babban tambaya ,
hakika bawai banason sanar dakai labarin mahaifinka bane sai
dai, bana son tuna baya, bana son tuna babban masoyina abin
kauna na" koda tazo nan a zancenta sai wasu kwalla na bakin
ciki suka gangaro bisa kuncinta.
.
Muhaisin ya kariso wajenda take sannan yace
"Ya ummina hakika kece kadai nake gani nakejin farin ciki a
cikin zuciyana, bana son ganin zubowan kwallanki, bana son
jin labarin muddin hakan zai tsaida zuban kwallanki"
.
Hamasiya najin haka sai ta tausaya ma muhaisin ainun ta sanya
hannu ta tallafo habarsa tace
"Yakai dana kasani Mahaifinka Gawurtaaccen Sarki ne Adali
mai jinkan talakawa,
Mahaifinka shike mulkin birnin Tehran .
Kamanninka dana mahaifinka sak babu banbamci, Sunansa
Sarki HINZUR IBN HUMAS"
.
Part B is Coming Soon
Marubuci:- Shuraih Usman
Hakkin mallaka (m) Shuraih Usman
Company:- Shuraih 99%
(c) shuraih Usman 2017
Typing:- shuraih 99%

ID Numbers

Open Library
OL26378843M

History Created September 24, 2017 · 2 revisions Download catalog record: RDF / JSON

September 24, 2017 Edited by Shuraihusman Edited without comment.
September 24, 2017 Created by Shuraihusman Added new book.